Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, ofishin jaksancin Japan ɗin a Tehran ya ce a jiya Asabar ce ministan harkokin wajen ya iso Tehran don fara ziyar tasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa daga cikin ayyukan da ministan harkokin wajen na Japan har da ganawa da shugaban ƙasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da kuma ministan harkokin waje mai barin gado, Muhammad Jawad Zarif
Kamar yadda kuma Mr. Motegi zai gana da sabon ministan harkokin wajen Amir-Abdollahian wanda ake sa ran zai maye gurbin Mr. Zarif ɗin.
Daga cikin batutuwan da ake sa ran za a tattauna kansu tsakanin ɓangarorin biyu har da batun alaƙa ta diplomasiyya da kuma harkokin kasuwanci a tsakaninsu.
Кasashen biyu dai sun kasance suna da alaƙa mai kyau a tsakaninsu tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a ƙasar ta Iran duk kuwa da ƙoƙarin da Amurka ta yi na mai da Iran ɗin saniyar ware.
342/